Latest post

Tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya Daniel Amokachi ya taya jaruman Kannywood Mansurah Isah da Sani Danja murnar cika shekara 12 da aurensu.







Sani Danja da Mansurah suna cikin 'yan fim na farko-farko da suka auren juna, kuma sakon da suka wallafa a shafin Instagram ya ja hankalin jama'a sosai ciki har da tsohon dan kwallon na Najeriya.


A cikin sakon da tsohuwar jarumar fina-finan na Hausa ta wallafa mai dauke da hoton mijinta, ta yi takaitaccen bayani game da rayuwar aurensu na zaman hakuri da kaunar juna.
Kalaman sun nuna yadda kamar a gidaje da dama, ma'auratan ke zaman hakuri duk da irin sabanin da ta ce suna samu a lokaci zuwa lokaci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawan samun rahotanni marasa dadin ji na yawaitar mutuwar aure a arewacin Najeriya da kuma kisa ko kaiwa juna hari tsakanin wasu ma'auratan, lamarin da ake alakantawa da rashin soyayya, hakuri da rashin bin tsari mai kyau wurin assasa auren.
Mansurah ta ce dukkaninsu suna da rauni, inda wani lokaci takan yi gaba da mijinta ba tare da ya saba mata ba, yayin da wani lokaci kuma ya ki cin abincinta har ya ki ba ta kudi idan ta tambaye shi.
"Ka ci gaba da hakuri da ni ka ci gaba da dauke kai a kan laififfuka na. Domin nasan ni mai laifi ce a gare ka. Rayuwa ba ka taba zama 100% komin yaya akwai inda ka kasa," in ji ta.
Amma ta ce sukan yi dariyar sabanin da suke samu saboda sun zama abokan juna. Kuma har yanzu suna son junansu kuma suna taimakon juna.

1 comments :

 
Copyright © 2015. Arewazone
Blogger Templates